Zaben jagora a kungiyar AU
January 30, 2017A zaman taron da kungiyar ta yi a baya cikin watan Yulin shekarar data gabata ta 2016 dai, ba a kai ga cimma nasarar zabar wanda zai gaji Nkosazana Dlamini Zuma ba wanda hakan ya sanya aka dage zaben. A yanzu 'yan takara guda biyar ne za su kara a zaben wadanda suka hada da ministar harkokin wajen kasar Kenya Amina Mohamed da tsohon firaministan kasar Chadi Mussa Faki Mahamat da kuma wani jami'in diplomasiya na kasar Senegal. Wani kuma batu na daban da shugabannin na Afirka za su yi nazari a kansa wanda yanzu haka aka soma samun sabani tsakanin kasashen shi ne na sake dawowar kasar Moroko a cikin Kungiyar ta AU wacce ta fice tun a shekara ta 1982, saboda kungiyar OAU a wancan zamani ta amince da shigar Jamhuriyar Saharawi cikinta. Yann Bedzigui daga wata cibiya da ke yin bincike a game da sha'anin tsaro watau ISS, kana kwararre game da kungiyar ta AU ga kuma abin da yake cewa:
Tilas abi dokokin AU
"Wannan magana ce ta zabi, Maroko na daga cikin kasahen da ke cikin nahiyar Afirka don haka daidai ne a maraito, amma abin da ke magana shi ne yin amfani da dokokin kungiyar gabannin sake karbar Marokon a cikin AU.''
Kaso 70 cikin 100 na kudaden da kungiyar ta AU kan samu na zuwa ne daga waje kuma ana ganin Marokon za ta iya zama wata kafa ga kungiyar ta samun karin tallafi a cewar Giles Olakounle Yabi wani masanin kimiyyar siyasa daga kasar Benin.
Ya ce.''Maroko kasa ce da ke samun habakar tattalin aziki tsahon shekaru masu yawa, gudunmawarta za ta iya yin tasiri ga kuniyar ta Tarrayar Afirka, sai dai kuma akwai bukatar ganin kungiyar ta daina yin irin wannan dogaro indai har tana son samun cikakken yanci.''
Tashe-tashen hankula a kasashen kungiyar
Wasu karin batutuwan da taron zai tabo sune batun tashin hankalin da ake fama da shi a Sudan ta Kudu da halin da ake ciki a Libiya inda mayaka masu jihadi ke cin karansu ba babbaka da batun masu ta'aadanci a Mali da Somaliya da kuma Najeriya, sai kuma rikicin siyasa na Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango da Brundi. Yayin da ake ganin kuma wata sabuwar muhawara za ta barke a taron tsakanin kasahen Burundi da Afirka ta Kudu da kuma Gambiya, wadanda suka fice daga cikin kotun kasa da kasa ta ICC a shekara ta 2016 da kuma Senegal da Bostwana da sauran kasashe masu goyon bayan kotun ta ICC.