Mutane da dama sun yi zaben Jamhuriyar Nijar
December 27, 2020Zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki da ya gudana a wannan Lahadi a Jamhuriyar Nijar inda jama’a da dama suka shaida cewa mutane sun fito dafifi a yankuna na kasar domin zaben wanda amma ‘yan adawa da masu mulki kowa na zargin dan uwansa da aikata sata a cikin zaben, abin da aka saba gani tsakanin 'yan siyasa.
A hakumance ya zuwa yanzu hukumar zabe ba ta bayyana alkalumma na adadin mutanen da suka fito zaben na wannan karo ba, a Zahiri take cewa a yankunan da dama jama'a sun fito dafifi domin kada kuri’ar tasu, kuma jam’iyyun siyasa sun dauki mataki na kasawa da tsarewa a runfunan zaben kamar dai yadda za ku ji a firar da ta hada ni da wakillan jam’iyyun siyasa a wata runfar zabe da na ziyarta a birnin Yamai.
Shugabannin runfunan zabe da dama a birnin Yamai dai sun tabbatar da cewa har ya zuwa yammacin Lahadi zaben ya wakana a cikin kwanciyar hankali kamar dai yadda daya daga cikinsu ya tabbatar mani.
Karin Bayani: Ana ci gaba da zaben Jamhuriyar Nijar
Sai dai duk da yadda a runfunna zabe da daman a birnin Yamai al’amurra suka dunga tafiya salin alin ‘yan adawa da masu mulki sun yi ta zargin junansu da aikata sata ko yunkurin yin hakan a cikin zaben nay au kamar dai yadda za ku ji daga bakin wasu magoya bayan adawa da na masu mulki da na yi kicibis da su bayan kada kuri’arsu a birnin na Yamai.
Da misalin karfe takwas ta daren wannan Lahadi ne dai ya kamata a rufe runfunan zabe a fadin kasar Nijar. Sai dai domin shawo kan matsalar jinkirin da ake samu wajen bude runfunan zabe a bisa wasu dalillai a wasu yankunan kasar wata doka ta hukumar zabe ta tanadi cewa ko ma a wani lokacin runfar zabe ta bude to ya zamo dole a gare ta ta kwashe awoyi 11 tana aiki Tun a daren wannan Lahadi ne dai ne dai hukumar zabe mai zaman kanta z ata soma kwanan zaune na soma tattarar sakamakon zaben na wucin gadi wanda ake sa ran hukumar zaben ta bayyana shi a cikin kwanaki biyar masu zuwa ga kotun tsarin mulkin wacce ita kuma za ta bayyana kammalallen sakamakon a cikin makonni biyu masu zuwa.