Zaben Jamus: Merkel ta sha kaye a mazabarta
September 5, 2016Jam’iyyar ta Alternative for Germany (Alternative für Deutschland, AfD) mai ra’ayin adawa da baki a Jamus an kafata a shekarar 2013, a shekarar dai ta samu sama da kaso hudu cikin dari, wanda ya kasance sauran kiris ta samu kaso biyar cikin 100, abin da zai ba ta dama ta shiga majalisar dokokin Jamus ta Bundestag. A wannan wata dai na Satimbar 2016 jam’iyyar na da wakilici a majalisun jihohi tara daga 16 na Jamus. Jam’iyyar AfD mai shekaru uku da kafuwa da yanzu ke samun jagoranci na Frauke Petry da Jörge Meuthen ta samu kashi 21 daga cikin dari na kuri'un jam'iyyar a jihar ta Mecklenburg-Western Pomerania da ke zama yankin da Shugaba Merkel ta fito mai mutane miliyan daya da dubu dari shida cikin al'ummar kasar miliyan 80. Sai dai duk da haka ana kallon burin jam'iyyar bai cika ba a zaben na ranar Lahadi, inda ta ke fatan zama jam'iyya mafi karfi a Mecklenburg-Western Pomerania, sannan ba ta samu sama da kaso 24 cikin 100 ba da ta samu a wata jihar da ke a Gabashi wato Saxony-Anhalt a zaben watan Maris. Sai dai Jörge Meuthen, ya ce burinsu ya tasamma cika:
"Wannan babbar alama ce ta zuwa Berlin a zabukan da ke tafe a makonni biyu masu zuwa, mu shiga majalisar jiha a karo na 10, kana alama ce ta nasara a zaben tarayya, babban burinmu shi ne mu yi jagoranci."
Sebastian Friedrich, masanin kimiyyar zamantakewa kuma kwararren masani kan jam'iyyar ta AfD ya ce burin na su Meuthen a jam'iyyar AfD a zaben 'yan majalisar tarayya da za a yi a shekara mai zuwa ta 2017, na iya cika sai dai akwai kalubale a gabansu. Koda yake sabanin yadda wasu masu kin bakin ke cewa janyo 'yan gudun hijira da Shugaba Merkel ke yi shi ya sa ta rasa magoya baya a jihar, Eva wacce ita ma ke zaune a birnin Schwerin fadar gwamnatin Mecklenburg-Western Pomerania bayyana fatanta ta yi a kan wannan jam'iyya ta AfD da kada ta yi karfi da zai mayar da Jamus baya a siyasar duniya.