Zaben Jamus na 2021: Kawancen jam'iyyu
Kuri'un jin ra'ayoyin jama'a sun nuna cewa babu kawancen jam'iyyu biyu da zai yi nasarar samun rinjaye bayan babban zaben ranar 26 ga watan Satumba. Ga takaitaccen bayani.
Alamu na launukan jam'iyyun Jamus
Ana gane jam'iyyar CDU da 'yar uwar tagwaitakarta ta CSU ne da launin baki. Yayin da launin ja ke a matsayin alamar jam'iyyar SPD kazalika ta masu ra'ayin gurguzu. Launin dorawa na wakiltar jam'iyyar FDP mai sassaucin ra'ayi. Jam'iyyar masu kare muhalli na bayyana kanta. Kafafan yada labaru na Jamus na amfani da hadakar launukan da tutocin kasa a matsayin hanyar hadin gwiwar siyasa.
Baki da ja da kore — launukan kawancen Kenya
Gwamnatin hadakar CDU da SPD sun yi mulkin shekaru takwas. Abin da ake kira "babban kawance" na manyan jam'iyyu, amma bisa alamu ba za su samu wannan rinjayen ba. Hadaka da jam'iyyar masu kare muhalli na iya tabbatar musu da rinjaye. Amma a yayin tafiyar kafada da kafada da CDU da SPD ke yi a yanzu, da wuya a fayyace mai karfi da za ta fitar da shugaban gwamnati.
Baki da ruwan dorawa da kore — launukan kawancen Jamaica
A baya, jam'iyyar CDU ta sha yin hadaka da karamar jam'iyyar FDP a matakan kasa da jihohi. Shigar da jam'iyyar masu kare muhalli a matsayin ta uku don kafa gwamnatin kawance, zai zama zabi ga yawancin 'yan jam'iyyar CDU. Sai dai tafiya da jam'iyyun FDP da masu kare muhalli zai kasance da wuya, kamar yadda yake a zaben 2017.
Baki da ja da ruwan dorawa — launukan kawancen Jamus
Gamayyar jam'iyyun CDU da SPD da kuma FDP. Wannan hadakar za ta iya samun kaso 50 cikin 100 na wakilan majalisar wakilai. Wannan zai zame zabi ga manyan 'yan kasuwa da masu manyan albashi. Amma idan SPD ce ke da rinjaye fiye da CDU, launukan za su sauya zuwa ja da baki da ruwan dorawa. Babban garambawul.
Launukan ja da ja da kore
Hadakar jam'iyyar SPD da ta masu rajin kare muhalli da ta masu sassaucin ra'ayi, fata ne da masu tsattsauran ra'ayi ke hasashe idan har ba su tabuka komai a zaben ba. Kawancen da zai samar da kashi 50%, idan har jam'iyyar masu sassaucin ra'ayin ta samu nasarar kaso 5% a majalisa. Amma alakarsu ba ta fiye kyau ba, saboda tsattsauran matsayar da masu sassaucin ra'ayin ke da shi kan manufofin ketare.
Ja da ruwan dorawa da kore — kawancen "traffic light"
A baya dai jam'iyyar FDP ta yi fatali da yiwuwar kawance da SPD da kuma masu rajin kare muhalli. Sai dai a wannan shekarar lamarin ya sauya. Jam'iyyar na muradin shiga a dama da ita a harkokin gwamnatin kasar ba tare da la'akari da wadanda ke cikin kawancen ba.