Zaben jihohi a Jamus: Nasara ga AfD, hasara ga gwamnati
September 2, 2024Jihohin Jamus biyu daga cikin jimillar 16 ne a ka gudanar da zaben sabuwar majalisar jiha a ranar daya ga Satumban 2024. Kuma an samu masu jefa kuri'a miliyan biyar kawai daga cikin fiye da miliyan 61 da ake da su a fadin Jamus. Amma, zaben jihohi Thuringia da Saxony sun ja hankali fiye da mahimmancin da yankunan ke da shi a kasar, saboda a karon farko, jam'iyyar da ke da tsattsauran ra'ayi a kan baki ta AfD ta samu fiye da kashi daya cikin uku na kuri'un da aka kada. Sannan a daya hannun, ba a taba samun jam'iyyun da ake damawa da su a gwamnatin tarayya a Berlin da suka taba samun sakamako marasa kyau kamar a wadannan tagwayen zabukan jihohi ba.
79% na Jamusawa ba su gamsu da gwamnati ba
A jihohin Saxony da Thuringia, jam'iyyar AfD mai tsattsauran ra'ayi ta samu ninki biyu na kuri'un da jam'iyyun SPD da Greens da FDP da suka kafa gwamnatin tarayya suka samu. Hasali ma dai, wannan sakamakon bai wadatar ma jam'iyyun FDP da Greens su shiga majalisun dokokin jihohin Saxony da Thuringia ba, amma jam'iyyar SPD ta shugaban gwamnati Olaf Scholz ta ceto kanta inda ta samu kujeru a majalisun jihohin.
Karin bayani: Fargabar nasarar AfD a Saxony da Thuringia
Ayar tambaya a nan ita ce: Wai shin wane darasi ne ke tattare da wadannan zabuka ga gwamnatin tarayya? Kashi hudu cikin biyar na Jamusawa ba su gamsu da kamun ludayin gwamnatin tarayya ba. Dama dai, a kididdigar jin ra'ayin jama'a na kafofin watsa labarai na gwamnati ARD, 'yan Jamus da yawan bsun ba da maki marasa kyau ga shugaban gwamnatin Jamusr Olaf Scholz da ministocinsa.
Korar baki kafin zabe bai taimaka wa gwamnati ba
Ana ganin gwamnatin hadin gwiwar ta Jamus a matsayin wacce da rarrabu kuma ba za ta iya tabuka komai ba. Shugaban jam'iyyar The Greens Omid Nouripour ya ce ya zama dole sun yi karatun ta nitsu don sanin alkiblar da za su dora gwamnati a kai. Daidai da matakan da fadar mulki ta Berlin ta dauka na tsaurara dokoki tsaro da shige da fice bayan hari da wuka da aka kai a Solingen jim kadan gabanin zaben jihohin ba su taimaka wa gwamnatin tarayya ba a wannan zabe. Maimakon haka, jam'iyyar AfD ta danganta korar masu laifi 28 zuwa kasarsu Afghanistan a matsayin tabbatar da abin da ta jima tana fada na illar da baki ke yi wa Jamus. Saboda haka ne shugabar AfD Alice Weidel ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi murabus.
Ya makomar gwamnatin kawance bayan zaben Brandenburg?
Makonni uku bayan zabukan Saxony da Thuringia, za a gudanar da zaben jihohi a jihar Brandenburg da ke gabashin Jamus a ranar 22 ga Satumba. Sai dai a wannan jiha ma, jam'iyyar AfD da ke kyamar baki na kan gaba a kididdigar jin ra'ayin jama'a, amma SPD ta shugaban gwamnati na biya mata baya. Saboda haka, jam'iyyar SPD za ta yi iya kokarinta don samun nasara. Duk da raunin da ya samu bayan zabukan jihohin Thuringia da Saxony, shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz na samun goyon bayan jam'iyyarsa, inda shugaban SPD Klingbeil ya jaddada cewa za su mara wa shiga gwaninsu baya domin ya samu wa'adi na biyu na mulki.
Karin bayani: Jamus: Jam'iyyar shugaban gwamnati ta sha kaye
Amma kawancen SPD da Greens da FDP zai ci gaba da kasancewa har lokacin zabe na gaba? A fili yake cewar rashin sakamako mai kyau a zabukan Jihohi da kuma irin guna-gunin da ake samu a Jamus na dagula wa gwamnati al’amura.