Hukumomi a Jamhuriyar ta Kamaru da masu sanya idanu na kungiyar kasashen Afirka ta AU sun ce zaben na ranar Lahadi ya gudana lami lafiya a mafi akasarin kasar, ko da dai an samu 'yan matsaloli nan da can, amma dai ba su yi yawan da za a ce za su iya yin wani mummunan tasiri ga sakamakon zaben da zai fita nan da makonni biyun da ke tafe ba. Ta bangaren tsaro kuwa, hukumar zaben Kamaru din ta ELECAM ta ce ba a fuskanci wani babban kalubale ba kamar yadda Erick Essouse darakta janar na hukumar ya shaidawa DW
Sai dai wani da ya sanya idanu kan zaben kana ya bukaci da a sakaya sunansa ya ce lamarin ba haka ya ke ba. Ya ce "A matsayina na mai sanya idanu na kasance makale cikin wata rumfar zabe na tsawo kimanin sa'o'i 4 saboda harbe-harbe da aka yi ta yi ba kakkautawa. Ban san ko su waye da waye suka yi taho mu gama ba don ina cikin dakin da ake kada kuri'a amma dai mutane da dama ba su samu damar isa rumfar zaben don kada kuri'unsu ba."