1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Macron, sabon babi na hadin kan Turai

April 25, 2022

Sake zaben Emmanuel Macron a matsayin shugaban kasar Faransa tamkar martani ne a siyasance ga harin da Rasha ke kai wa kasashen yammacin Turai kuma sabon wa'adi ne na ci gaba da aikin hada kan Turai.

https://p.dw.com/p/4AQ24
Frankreich Präsidentschaftswahl Wahlsieger Macron
Hoto: BENOIT TESSIER/REUTERS

Sake zaben Emmanuel Macron a matsayin shugaban kasar Faransa tamkar dai martani ne a dimokuradiyyance na harin da Rasha ke kai wa kasashen yammacin duniya musamman na Turai. Sannan kuma wani wa'adi ne na ci gaba da aikin hada kan Turai, in ji Frank Hofmann a sharhin da ya rubuta wanda Mohammed Awal Balarabe ya fassara.

Kusan kashi 60% na 'yan Faransa sun kada kuri'ar sake zaben Emmanuel Macron, tare da juya baya ga mai kyamar baki Marine Le Pen wacce ta samun fiye da kashi 40% na kuri'un da aka kada. Amma za ta ci gaba da tallata manufofinta na neman fitar da Faransa daga Kungiyar tsaro ta NATO tare da juya wa Kungiyar Tarayyar Turai baya.

A watan Yuni ne dai za a gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin kasar ta Faransa. Sai dai duba da kashi daya cikin uku na kuri'u da masu kyamar baki suka samu a zagayen farko da kuma kashi 20% na kuri'un da masu ra'ayin gurguzu na Jean-Luc Mélenchon suka samu, abin da ya fito sarari shi ne 'yan Faransa na son ganin sauyi a kasa. Dama dai farin jinin 'yan siyasa na Paris ya dade da raguwa sakamakon bambanci da ke akawai tsakanin bukatun talakawa da abubuwan da suke aiwatarwa. Kuma wannan gargadi ne ga tsarin dimokuradiyya a kasar.

Frankreich Präsidentschaftswahl Wahlsieger Macron
Hoto: BENOIT TESSIER/REUTERS

Jam'iyyar La République en Marche mai sassaucin ra'ayi da Macron ya kafa ta kara ta'azzara gibin dimokuradiyya a cikin shekaru biyar da suka gabata, wanda kuma ya kara tsananta sauyin sheka daga jam'iyoyin da ke da ra'aayin mazan jiya da ta masu ra'ayin gurguzu. Dole ne Macron da mukarrabansa su canza kamun ludayinsu idan Faransawa ba sa so kasarsu ta fada hannun masu tsanancin kishin kasa.

Wannan dai ba ya rasa alaka da bakin jinin da Kungiyar Tarayyar Turai gaba daya ta yi musamman ma kasar da ta fi karfin tattalin arziki a cikinta wato Jamus. A Faransa dai, ana daukar EU a matsayin hadakar manyan kamfanoni, amma ba a matsayin kungiya da ke kare al'ummarta a cikin gida da waje ba. Ko da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine cikin watanni biyun da suka gabata ya nuna cewa da yawa sun yi gaskiya a wannan batu, domin yakin Rasha dai wani hari ne ga nahiyar Turai da ke da muradin tabbatar da ‘yanci da yada dimukaradiyya. 

Sai dai har yanzu ba a samun rinjayen da zai bayar da damar yanke shawara a Brussels kan batutuwan manufofin ketare na EU cikin sauki ba. Firayiminista Viktor Orbán na Hangari da ke dasawa da Putin ga misali na iya hawa kujerar na ki don aiwatar da wata shawara- alhali Rasha ta kai hari da makamai a kan wata kasa da ke bin tafarkin dimokuradiyya a Turai. Yawancin Faransawa na ganin wannan a matsayin shirme.

Frankreich Präsidentschaftswahl | Wahlsieg Macron
Hoto: Thibault Camus/AP/picture alliance

Sakamakon zaben Faransa ya zama dama ta biyu ga Turai musamman ma ga Jamus. Macron ya kwashe shekaru biyar yana neman daidaita kungiyar Tarayyar Turai a matsayin babbar kungiyar kasashen duniya tsakanin Amirka da China, a karkashin hadin gwiwar Faransa da Jamus. Sai dai abin takaici shi ne, tsohuwar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ba ta son yin koyi da shi. A fili yake cewa gadon manufofin Turai na Merkel yana da rauni idan aka kwatanta da na wadanda suka gabace ta kamar Helmut Kohl ko Helmut Schmidt.

A yanzu dai gwamnatin hadaka ta SPD da Greens da FDP a Berlin na da damar gyara wannan kuskure. Dama 'yan jam'iyyar The Green sun yi dabarar karfafa manufofin EU cikin yarjejeniyar kafa gwamnati. sabanin yadda SPD ta saba dari-dari wajen goyon bayan Turai, ta yi shawarwari na musamman a fannoni daban-daban na siyasa. Ya kamata Turai ta dauki babban matakin dunkule kasashen Turai shigen na Amirka. Wannan shi ne abin da ya kamata a sa gaba, kuma wuka da nama sun kasance a hannun fadar mulki ta Berlin tun ranar Lahadi.