Zaben Najeriya na tasiri a Jamhuriyar Nijar
February 25, 2023Wasu daga cikin masu harakokin kasuwanci da hada-hada tsakanin Nijar da Najeriya sun dauki matakai na rigakafi tun kafin ranar zabe. amma bai hana yin tasiri kan harkokin yau da kullun musamman ga mazauna birnin Maradi ba.
Alhaji Yahaya Ali da ya mallaki motocin dakon kayan 'yan kasuwa daga Kano zuwa Maradi, ya ce komai nasu ya tsaya cik sakamakon zabe na tarayar Najeria. Shi kuwa Kabirou Mouktar mai sayar da dusa da takin zamani, ya ce yanzu haka kayanshi na kan iyaka saboda dokar rufe boda.
A wasu cibiyoyin hada-hada da zirga zirga, ra'ayoyin wasu 'yan kasuwa da direbobi da 'ya canji sun banbanta kan tasiri da zaben Najeriya ya yi a harkokinsu. Alhaji Rabi'ou da ke sayar da kayan abinci ya ce zaben Najeria mai dogon zango ne saboda matsayinta a Afirka