Jam'iyyun hamayya sun nemi a sake zabe
February 28, 2023A yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zabe na shugaban kasa da 'yan majalisun tarraya a Najeriya, sakamakon da ke fitowa a yanzu na janyo ka-ce-na-ce a tsakanin jam'iyyun hamayya da masu goya musu baya a kasar.
Ya zuwa wannan Talatar, jam'iyyar APC mai mulki ce take sahun gaba bayan sakamako na jihohi 14 da hukumar zaben tarrayar Najeriyar ta bayyana. APC dai ta lashe jihohi guda shida a yayin da takwararta ta PDP tai nasara a jihohi guda biyar, Labour party ta samu jihohi guda uku.
To sai dai kuma tun ba a kai ga ko ina ba, sakamakon ke janyo daga hakarkari tsakanin masu takarar da ma 'yan kallon ciki dama wajen tarrayar Najeriyar.
Wata wasikar tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo dai na shirin komawa zuwa kanwa uwar gami a siyasar in da masu adawar suke fadin ba dama. Obasanjon, ya zargi jami'an zabe na kasar da hadin baki da gwamnoni na jihohi wajen kai wa ya zuwa sakamakon da bai zama na sahihi.
Tuni dai bangare na jam'iyyar PDP ta adawa ta sa kafa ya shure sakamakon, amma kuma a yayin da masu adawar suke fadin akai ga kasuwa, shi kansa ofishin yakin neman zaben APC ya ce, kama daga shi kansa tsoho na shugaban kasar ya zuwa masu adawar na hawaye na kawai na yaudara a cikin tsarin da ya tabbatar da sahihanci a ko'ina.
A karon farko, ana kallon faduwa ta gwamnonin da ke da fatan rikidewa ya zuwa dattawan majalisa, 'yan kungiyar babu dai daya a cikin gwamnonin G5 na cikin jam'iyyar PDP alal ga misali da yai nasarar lashe zaben shiga majalisar dattawa.
Su kansu gwamnoni irin nasu Taraba da Kebbi da ma Cross Rivers dai sun sha kaye a wani abun da ke zaman ba sabun ba cikin fagen na siyasar kasar. Ana ma kallon yiwuwar samun majalisun tarrayar da ke bukatar hada karfin jam'iyyu kafin iya kai wa ga tabbatar da samun rinjaye a karon farko tun bayan gina jamhuriya ta hudun da ke gudana yanzu a fadar masana kamarsu Faruk BB Faruk da ke sharhi cikin batun na siyasa.