Zaben Najeriya ya dauki hankalin jaridun Jamus
February 17, 2023Jaridar Der Tagesspiegel ta mayar da hankali kan zaben da ke tafe a Najeriya, inda ta ce idan aka gudanar da zabe a ranar 25 ga watan Fabrairu kamar yadda aka tsara, wannan zai zama wani labari mai dadi. Dalili kuwa shi ne, shekaru hudu da suka gabata, INEC ta dage zaben majalisar kasa sa'o'i kadan kafin a bude runfunan zabe saboda sojoji ba su tabbatar da ingancin tsaro ba. A wancan lokaci dai an fuskanci barazanar ta'addanci daga mayakan Boko Haram masu kishin Islama.
Jaridar ta kara da cewa bai kamata a ce kalubalen tsaron ya faru a zaben bana ba, inda shirn gudanar da zaben shugaban kasa ke gudana yadda ya kamata. Amma mako guda kafin a kada kuri'u a kasar da ta fi kowacce yawan jama'a a Afirka, fargabar barkewar rikici na haddasa zaman dar-dar. Baya ga tashin hankali da ke karuwa a yankuna da yawa na Najeriya, tarin matsaloli na gaban hukumar zabe mai zaman kanta INEC, wacce aka kai wa cibiyarta harin a makonnin da suka gabata, lamarin da ya yi sanadin mutuwar jami'anta biyu a tsakiyar watan Disamba.
Ita kuwa Die Welt ta yi sharhinta kan talauci a wasu kasashen Afirka mai taken: Ya kamata Turai ta kasance a Afirka. Ta ce Mozambik da ke kudancin Afirka na daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya bisa kididdigar Majalisar Dinkin Duniya. Fadin Mozambique ya ninka girman Jamus sau biyu, alhali kusan mutane miliyan 30 ne kawai ke rayuwa a kasar. Kusan kashi 40% na 'yaan kasar ba su iya karatu ko rubutu ba. kuma lokacin da Turawan mulkin mallaka na Portugal sun bar kasar a 1975, kashi 5& ne kawai na al'ummar Mozambiyk suka iya yi magana da harshen Portuguese.
Die Welt ta ce a wasu kasashen Afirka, Chaina ta ba da rancen gina filayen wasan kwallon kafa da layin dogo da tashar jiragen ruwa, yayin da Mozambik ta gina gadar Katembe mai tsayin mita 680 a babban birnin kasar Maputo. Jaridar ta ce bai kamata Jamus da Kungiyar Tarayyar Turai su yi sakaci da manufofin a Afirka ba, maimakon haka ma dole ne sun yi kyakkyawan tayin raya kasa ga gwamnatin Mozambique domin Kada ta ci gaba da samun rauni, amma ta ci gaba da karfafa.
A daya bangaren jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta mayar da hankali kan muhawara bisa janye sojojin Jamus na Bundeswehr daga kasar Mali da ke yankin yammacin Afirka a wannan shekara ba tare da jiran zuwa karshen shekara ba. Jam'iyyar adawa ta CDU/CSU ta hannun mai magana da yawun jam'iyyar Florian Hahn kan manufofin tsaro ya ce aikin dakarun na cikin ayyukan Majalisar Dinkin Duniya da suka fi hadari a duniya. Tun farko majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta amince ci gaba da aikin dakaru a Mali domin karfafa tsaro tare da janyewa sannu a hankali. A cewar Jam'iyyar SPD mai mulki janyewa zuwa watan Mayun shekara mai zuwa ta 2024, haka zai taimaka domin janye dakarun cikin tsanaki kuma bisa tsari.
Sannan Frankfurter Allgemeine Zeitung ta tunatar da cewa tun shekara ta 2013 aka tura sojojin Jamus na rundunar Bundeswehr zuwa kasra ta Mali domin yaki da tsageru masu kaifin kishin addinin Islama, inda kimanin sojojin 1,100 ke aiki, amma tun bayan juyin mulki aikin dakarun na Majalisar Dinkin Duniya ya shiga tsaka mai wuya kasashe masu tasiri irin Faransa da Birtaniya sun janye dakarunsu.