Zaben sabon shugaban ANC ya mamaye jaridun Jamus
December 22, 2017A labarin da ta buga jaridar Berliner Zeitung ta fara ne da cewa babban taron jam'iyyar ya hana darewarta a yanzu. Jaridar ta ce fiye da watanni shida jam'iyyar da ke zama daya daga cikin dadaddun kungiyoyin kwatar 'yanci a Afirka ta kwashe tana fama da gwagwarmayar wadanda za su jagorance ta. Amma zaban Cyril Ramaphosa a matsayin sabon shugabanta ya sa jam'iyyar ta kauce daga fadawa wani bala'i. Kuma ga jam'iyyar ta ANC babban taron nata karo na 54 a tarihin kafuwarta na shekaru 106 babbar nasara ce. Ko da yake Cyril Ramaphosa ka iya zama wani shugaba na gari ga Afirka ta Kudu, idan ANC ta sake lashe zabe a shekarar 2019, amma ba tabbas ko zai iya ceto kasar daga cikin mawuyacin halin da take ciki.
Ita ma a labarinta dangane da siyasar Afirka ta Kudun, jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa ta yi da ma 'yan kasuwar Afirka ta Kudu sun yi fatan samun wannan sakamako, domin jim kadan bayan zaben Ramaphosa a matsayin shugaban jam'iyyar ANC, darajar takardun kudin Afirka ta Kudu ta tashi a kan dalar Amirka, sannan kwana guda baya ta yi tashin da ba ta taba yi ba tun a cikin watan Maris. Kasancewarshi hamshakin dan kasuwa kuma mai matukar adawa da cin hanci, ana kyautata fatan zai share wa 'yan Afirka ta Kudu hawaye, musamman yadda matsalar cin hanci da rashawa ta yi katutu a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar ANC.
Daga siyasar Afirka ta Kudu sai ta kasar Yuganda, inda a sharhin da ta rubuta jaridar Die Tageszeitung ta fara da cewa burin Shugaba Yoweri Museveni na yin mulki har sai Mahdi ka ture ya tabbata. Sai dai tambaya a nan ita ce ko za a iya samun sauyin mulki cikin ruwan sanyi a kasar ta Yuganda? Wannan dai a cewar jaridar wani batu ne na makomar kasar. Abin da ke a fili shi ne yanzu Shugaba Museveni zai yi mulki da idan an hada gaba daya zai kai tsawon rabin karni wato shekaru 50 ke nan. Majalisar dokokin kasar ce ta yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima da ya ba wa shugaban mai shekaru 73 damar sake yin takara bayan ta soke dokar da ta takaita yawan shekarun 'yan takara a kasar. Shi dai Museveni wanda tun a 1986 yake jan ragamar mulki, yana iya tsayawa takara har sau biyu nan gaba. Jaridar ta kwatanta wannan matakin da majalisar dokokin kasar ta Yuganda ta dauka da wata kyautar bikin Kirsmetti ga Shugaba Museveni.