Zaben shugaban kasa zagaye na biyu a Girka
December 23, 2014Talla
Firaministan kasar Antonis Samaras, wanda wa'adin mulkinsa ke karewa a tsakiyar shekara ta 2016, ya ce a shirye yake ya sanya 'yan majalisu masu akidar Turai cikin gwamnatinsa idan har suka zabi dan takararsa Stavros Dimas, tare da alwashin shirya zaben 'yan majalisun daga shekara mai zuwa ta 2015. Sai dai ana ganin akwai wuya Firaministan ya iya samun rinjaye na kuri'un 'yan majalisu 200 wadanda za su ba da damar zaben dan takararsa, ganin yadda a zagaye na farko ya samu kuri'u 160 daga cikin kuri'un 'yan majalisun 300 da ke wannan kasa.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Suleiman Babayo