1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin hadakar Jamus na cikin garari

Mohammad Nasiru Awal ZMA
October 28, 2019

Sakamakon zaben 'yan majalisar dokokin jihar Thuringia ta gabashin Jamus da aka gudanar a ranar Lahadi na zama babban naushi ga jam'iyyun CDU da SPD.

https://p.dw.com/p/3S4pN
Deutschland Landtagswahl in Thüringen | TV Wahlstudio
Hoto: Imago-Images/K. Hessland

Jam'iyyun guda biyu wato CDU da SPD da ke tafiyar da mulki a gwamnatin kawance tarayyar Jamus sun yi asarar kuri'u a zaben na jihar Thuringia, yayin da jam'iyyar Die Linke ta zo ta farko ita kuma jam'iyyar masu kyamar baki ta AfD ta zo matsayi na biyu. Sai dai za a fuskanci babban kalubale wajen kafa gwamnati.

A zaben na 'yan majalisar dokokin jihar ta Thuringia da ya biyo bayan zabubbuka na 'yan majalisun dokoki a wasu jihohi biyu na gabashin Jamus a makonnin baya, na zama zakaran gwajin dafi ga farin jini ko kuma bakin jinin manyan jam'iyyun kasar ta Jamus.

A zaben dai Firimiyan jihar Thuringia kuma dan jam'iyyar Die Linke ta masu ra'ayin gaba dai gaba dai na gurguzu, Bodo Ramelow ana iya cewa sakamakon ya zo masa da kyau domin jam'iyyarsa ta samu kashi 31 cikin 100 abin da a karon farko ya ba ta matsayi mafi karfi a wani zabe. Lokavcin da yake jawabi a gaban magoya bayansa Ramelow ya ce sakamakon ya ba wa marada kunya.

Ya ce: "Shekaru biyar da suka gabata ba su zatab za mu kai labari ba, cewa suka yi gwamnatinmu za ta ruguje bayan kwanaki 100 amma yau shekaru biyar baya muna nan daran-dakau muna kuma jan akala."

Landtagswahl Thüringen 2019 | Bodo Ramelow
Firimiyan jihar Thuringia Bodo RameloHoto: Getty Images/S. Gallup

Jam'iyyar nan ta AfD mai akidar kyamar baki ita ce ta zo ta biyu da kashi 23 cikin 100 wato ta ninka har sau biyu yawan kuri'un da ta samu a baya. Yayin da CDU ke da kashi 21.8 wato ta rasa kashi daya bisa uku na kuri'unta ita kuma SPD ta yi faduwar ba nauyi da kashi 8.2 cikin 100. The Greens da kuma FDP kowace ta samu kashi 5.

Yanzu haka dai gwamnatin kawance tsakanin Die Linke da SPD da kuma Greens ta Firimiya Ramelow na jihar Thuringia, ta rasa rinjaye, kuma batun kafa gwamnati a jihar zai yi wahalar gaske, a cewar Mike Mohring shugaban jam'iyyar CDU a jihar.

Ya ce: "Sakamakon bai yi mana dadi ba kasancewa manyan jam'iyyu da ke taka rawa a tsarin dimukuradiyya ba. Ba mu yi tsammanin shiga wannan hali ba. Tun shekarar 1949 ba a taba gudanar da wani zabe bisa tsarin dimukuradiyya da aka samu irin wannan sakamakon ba, inda ba zai yiwu a kafa gwamnati da jam'iyyun masu matsakaicin ra'ayi ba."

Mike Mohring
Mike Mohring shugaban jam'iyyar CDU a jihar ThuringiaHoto: picture-alliance/dpa/M. Schutt

Dr. Gero Neugebauer masanin kimiyyar siyasa ne a birnin Berlin a hira da DW ya ce sau dawa manyan jam'iyyun da ke kulla kawance kan manta da cewa su kansu suna gasa da juna ne?

Ya ce: "Sakamakon zaben na Thuringia na nuna cewa yanzu a Jamus an yi bankwana da zamanin da babbar jam'iyyar za ta kama hannu karamar jam'iyya ta kulla kawance da ita. Matsala da ke akwai ita ce jam'iyyun da ke kulla kawance don adawa da AfD, sun kan manta cewa su kansu masu adawa ne da juna, wato ba sa kokarin zama zabi ga jama'a, shi ya sa masu zabe ke jefa wa jam'iyyar adawa kuri'u saboda rashin gamsuwa da aikin gwamnatin da ke jan ragamar mulki."

Masanin ya ce dole ne manyan jam'iyyun siyasar Jamus kamar CDU da SPD sun aiwatar da sauye-sauye a cikinsu musamman sauraron koken jama'a matukar suna su karya lagwan masu matsanancin ra'ayi da kyamar baki irinsu AfD.