1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na tallafa wa Sudan da Kenya

Mohammad Nasiru Awal AH
February 28, 2020

Batun zaben 'yan majalisun dokoki hadi da kuri'ar raba garda kan kundin tsarin mulki Guinea da kuma nasarar da Shugaban Togo Faure Gnassingbe ya samu a zabe sun dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/3YbeC
Guinea Wahlen in Conakry
Hoto: Getty Images/AFP/C. Binani

Bari mu fara da jaridar Die Tageszeitung wadda ta leka kasar Guinea inda a wannan Lahadin ake gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki hadi da kuri'a raba gardama kan yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, a wani lamari da jarida ta ce yana dab da jefa kasar cikin wani rikici na basasa. Ta ce tun a wasu shekaru da suka gabata al'umar kasar ke zanga-zangar rashin muhimman abubuwa ga rayuwa kamar ruwa da wutar lantarki, makarantu da asibitoci ga kuma rashin aikin yi da kuma bugu da kari karancin abinci da kuma rashin zabe mai tsabta, sai kuma a karshe matakan ba sani ba sabo da 'yan sanda ke dauka kan jama'a. Tun wasu watanni ke nan kasar ta Guinea da ke zama daya a jerin kasashen duniya masu fama da matsalar talauci, al'umar kasar ke nuna takaicinsu a kan siyasar shugaban kasa Alpha Conde musamman yadda yake wasa da dokokin kasa. Ko da yake Conde wanda a mako mai zuwa zai cika shekaru 82, wanda kuma tun a 2010 ya zama zababben shugaban kasa na farko a Guinea,  bai fito fili ya nuna ko zai sake tsayawa takara ba, amma 'yan adawa sun ce ai dama biri ya yi kama da mutum, saboda haka ne ya shirya kuri'ar raba gardama don yi wa kundin tsarin mulki garambawul.

Shugaba Faure Gnassingbe Eyadema wanda bai cika yin magana ba ya yi jawabi bayan samun nasara a zaben shugaban kasa 

Wahlen in Togo Faure Gnassingbe
Hoto: AP

Idan muka leka kasar Togo kuwa  jaridar ta Die Tageszeitung ta ce  biyo bayan lashe zabe da Shugaba Faure Gnassingbe ya yi, shugabancin kasar Togo zai ci gaba da zama hannun iyalin gidansu. Jaridar ta ce shugaban bai yi yawan magana ba ne hasali ma tun darwearsa kan kujerar shugaban kasa a Togo a 2005, bayan rasuwar mahaifinsa Gnassingbe Eyadema, bai taba yin hira da 'yan jarida ba. Bayan sake yin nasara a zaben na ranar Asabar, Gnassingbe mai shekaru 53 ta shafinsa na Twitter ya gode wa al'umar kasar.

Shugaba Frank-Walter Steinmeier na Jamus na kokarin ganin an tabbatar da dimukaradiyya a wasu kasashen Afirka inda ya kai ziyara

Bundespräsident Steinmeier im Sudan
Shugaban Kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier tare da firaministan Sudan Abdalla HamdokHoto: picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka

Ita kuwa jaridar Die Welt tsokaci ta yi kan ziyarar aiki da shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier ya kai wannan mako a kasashen Kenya da Sudan. Ta ce a ranar Alhamis Steinmeier ya isa kasar Sudan a mataki na biyu na ziyarar a Afirka bayan ya kammala ziyara a kasar Kenya. Jaridar ta kara da cewa Sudan na kokarin girke tsarin dimukuradiyya. Shugaban na Jamus ya gane wa kansa yanayin siyasa da kuma kokarin al'ummar kasar na bude sabon babi bayan shekaru gommai na shugaban mulki kama karya Omar al-Bashir. Jaridar ta ce ziyarar na zama karin kusantar juna tsakanin Jamus da Sudan, bayan da a tsakiyar watan Fabrairu gwamnatin tarayyar Jamus ta sake farfado da aikin hadin kai tsakanin kasashen biyu bayan shekaru 30 da dakatar da shi. Jamus nan-take ta ba wa Sudan Euro miliyan 80 ga fannonin ilimi, noma, makamashi da kuma tallafa wa matasa da mata. Sudan da ke da muhimmanci wajen samar da kwanciyar hankali da lumana a gabashin Afirka, tana matukar bukatar taimako, inji jaridar.