1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan takara guda a Zaben Turkiyya ya janye

May 11, 2023

Daya cikin 'yan takaran shugaban kasar Turkiyya da za su kalubalanci shugaba mai ci Recep Tayyip Erdogan ya sanar da janye takararsa, yayin da ya rage kwanaki uku a gudanar da zaben kasar.

https://p.dw.com/p/4RDlm
Hoto: AFP

Muharrem Ince na jam'iyyar Memleket daya cikin 'yan takara hudu masu adawa da manufofin Shugaba Erdogan ya sanar da janye takarasa a zaben da ke tafe ne a yayin wani taron manema labarai, inda ya sanar da dalilansa na daukar wannan mataki.

Kafin dai ya janye takarar tasa mista Muharrem Ince ya fuskanci kalubale na marabis din wasu jigajigai a jam'iyyarsa wace wani hasashen jin ra'ayin jama'a ya nunar da za ta iya samu kaso biyu zuwa hudu cikin dari na kuri'un za a kada a ranar 14 ga wannan wata na Mayu da muke ciki.

A cewar cibiyar Metropoll institut da yi fice wajen hasashen jin ra'ayin jama'a, janye takarar da Muharrem Ince ya yi abin murna ne ga dan takara Kemal Kiliçdaroglu domin hakan zai kara masa karfi a hamayar da yake da shugaba mai ci Erdogan wanda farin jininsa ke kara yin kasa a wajen al'ummar Turkiyya.