1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Turkiyya: Zangon kasa ga K.Kiliçdaroglu

May 27, 2023

Dan takarar da zai kalubalanci shugaba Recep Dayyip Erdogan a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Turkiyya na zargin gwamnati mai ci da yi masa zagon kasa a yayin yakinsa na neman zabe.

https://p.dw.com/p/4Rt3S
Hoto: Tunahan Turhan/Sopa/Zuma/picture alliance

Kemel Kiliçdaroglu ya ce an toshe masa hanyoyin aike sakonnin kar ta kwana na SMS wa magoya bayansa da kuma sauran al'umman kasar yayin da ya ke zawarcin kuri'unsu domin kowo kashen mulkin sai mahadi ka ture na shugaba Erdogan.

Dama dai a wannan Jumma'a kungiyar 'yan jarida Nagari na kowa ta Reporters sans Frontières ta nuna takaicinta kan rashin samar da daidaito wajen baiwa 'yan takarar biyu damar tallata munufofinsu a kafafen sadarwar kasar tana mai zargin shugaba mai ci Recep Dayyip Erdogan da yin kakagida a gidajen talabijin din kasar. Kungiyar ta kuma ce wannan wani yunkuri ne na yin magudi kana kuma yin karan tsaye ga dimukuraddiya tare da toye wa al'ummar Turkiyya hakkinsu na zaben shugaban da ya kwanta masu a rai.