Zaben 'yan majalisa a jihohi uku a Jamus
March 13, 2016A ranar Lahadin nan kimanin masu kada kuri'a miliyan 12 ke gudanar da zaben 'yan majalisa a wasu jihohi uku na Jamus wato Baden-Württemberg da Rhineland-Palatinate da ke a Kudu maso Yammaci da Saxony-Anhalt da ke a Gabashi. Zaben da irinsa bai cika daukar hankali ba a lokutan baya, sai dai a wannan karo saboda zura idon al'umma na kasar ta Jamus da ma wasu kasashe na waje, ana dako aga yadda za ta kaya ganin yadda batun 'yan gudun hijira da shugabar gwamnati Angela Markel ta yi ruwa ta yi tsaki a kansa, ya zama shi ne abin da ake duba, wanda kuma shi ake ganin ta yiwu ya sanya jam'iyyar CDU ta Markel din ta sha mamaki. Sai dai wasu na ganin ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare.
Da take karkare nata kamfe a ranar Asabar a jihar Baden-Württemberg Merkel ta sha alwashin maida 'yan gudun hijira masu kwarara Jamus saboda dalilai na tattalin arziki gida. Sai dai ta sake jaddada aniyarta ta bada kariya ga 'yan gudun hijira da suka shiga kasar saboda dalilai na neman jinkai.