1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bobi Wine na neman kotu ta soke zaben Yuganda

Binta Aliyu Zurmi MNA
February 1, 2021

Robert Kyagulani wanda ake wa lakabi da Bobi Wine ya shigar da kara a kotu domin neman a soke zaben da ya gudana a watan Janairu a kasar.

https://p.dw.com/p/3ofjG
Uganda Wahl Robert Kyagulanyi Bobi Wine
Hoto: Sumy Sadruni/AFP/Getty Images

Madugun adawar kasar Yuganda Robert Kyagulani wanda ake yi wa lakabi da Bobi Wine ya shigar da kara a gaban kotu domin neman a soke zaben da ya gudana.

A lokacin da yake bayani a Kampala babban birnin kasar, lauyan jam'iyyar adawa ta NUP ya ce suna bukatar a soke wannana zaben bisa kurakuren magudi da aringizon kuri'u da uwa uba na rikicin kame 'yan adawa.


Sakamakon zaben dai, ya ba wa shugaban kasar Yoweri Museveni wanda ke kan karagar mulki tun a shekarar 1986 nasarar zarcewa a wani sabon wa'adi na shidda, yayin da Bobi Wine ya zo a matsayi na biyu.