Yuganda: Zabtarewar kasa ta kashe mutum 34
October 12, 2018Talla
Zabtarewar lakar a sanadiyar mamakon ruwan sama ta binne tarin gidaje da kuma dabbobi, akwai kuma mutane da yawa da ba a ji duriyarsu ba tun faruwar lamarin. Hukumomi sun bazama aikin ceto rayuka tare da tallafawa wadanda suka tsira da rayukansu. Yankin na gabashin kasar Yugandan da ke kan iyaka da kasar Kenya ya sha fama da wannan matsala a shekarun baya.