Zafi na hallaka 'yan gudun hijira
August 12, 2015Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ya zuwa yanzu yara kanana 63 ne suka rasa rayukansu sakamakon matsanancin zafin da ake yi a yankin gabas ta tsakiya, ta na mai kashedin karuwar adadin wanda za su rasu muddin dai ba a gaggauta kaiwa 'yan gudin hijirar dauki ba.
A sansanin Azraq da ke kasar Iraqi, yankin da zafi ya kai maki 56 a ma'aunin celcius a 'yan kwanakin nan yara kanana 2 aka bada sanarwar sun rigamu gidan gaskiya sakamakon matsanancin zafin. Mazauna yankin da ke fama da daukewar wutar lantarki su kan fake da jika kansu da ruwan da motocin dakon ruwa ke kawo musu to sai dai lamarin ya kara munana bayan da motocin suka daina kai musu ruwan.
Haka ma abin ya ke a sansanin Arsal da ke kasar Lebanon inda nan ma matsanancin zafin ya yi wa yara uku sanadin hallaka. Mazauna wannan sansanin dai sun roki Majalisar Dinkin Duniya da ta gaggauta agaza musu. Da fari an bijiro da wani tsari na tallafawa wadannan mutane sai dai daga baya an fuskanci tsako. Wani mutum da abin ya shafa ya shaidawa DW cewa "an sanya sunana da na 'ya'yana goma cikin wadanda za a dinga amma tun da aka fara wannan matsanancin zafin,ba abin da aka kawo mana''
Hukumar kula da 'yan gudun hijirar dai ta ce karancin kudin da ta ke fama da shi ne ke tilasta wajen rashin cimma abinda ta sanya a gaba baya ga karuwa da ta ce an samu na yawan 'yan gudun hijira a yankin kasashen Larabawa. Yanzu haka dai yawan 'yan gudun hijirar sun kai miliyan shidda kuma suna warwatse ne a kasashe daban-daban.