1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen na cikin yanayin zafi

Abdoulaye Mamane Amadou SB/AMA
July 18, 2023

A wasu kasashen Turai tsananin zafin da ake fama yi ya ninka har sau biyu a cewar masana, idan aka yi la'akari da yadda ya kasance a shekarun baya, kana haka batun yake a wasu kasashen kamar Kanada da Amirka da China.

https://p.dw.com/p/4U4q1
Turkiyya I Yanayin zafi
Zafi a kasar TurkiyyaHoto: Tolga Ildun/ZUMA/dpa/picture alliance

 

Da maki 52,2 na ma'aunin zafi na selshiyos ne yankin Xinjiang da ke yammacin China ya wayi gari, lamarin da ka zama irinsa na farko a tarihin yammacin kasar mai makwabtaka da wasu kasashen tsakiyar Asiya.

Suma wasu kasashen nahiyar Turai sun soma wannan makon da tsananin zafin da ya wuce kima, ana hasashen ma'aunin zafi a tsibirin Sardaigne na Italiya ka haura fiye da maki 48, a yayin da birnin Roma ya kai maki 42 a cewar hasashen, ita kuwa Spain na ke shirin fuskantar maki 44 ne in ji hasashen yanayin, sai dai ga kwararre JOAN BALLESTER da ya yi nazari kan mace-macen masu da nasaba da tsananin zafi, cewa ya yi kasashe hudu ne suka fi shafuwa a wannan karo na Italiya, Portigal, Spain da kuma Girka.

Sararawa lokacin zafi
ZafiHoto: Tolga Ildun/ZUMA/dpa/picture alliance

Dumbun mutane na amfani da ruwa mai sanyi da sauran ababen kare kai daga zafin ranar da ake kwallawa a yankuna da dama na Turai, hukumomi na kokarin wayar da kan jama'a baya ga daukar matakan kare kai daga mawuyacin hali, ga misali a kasar Girka ma'aikatan sa kai na bayar da ta su gudunmawa ga mabukata, irin su Anastasia Morou ta hukumar agaji ta Red Cross.

Fiye da mutane dubu 60 ne suka halaka a shekarar bara a nahiyar Turai sakamakon iftila'in na tsananin zafi, lamarin da ya kai su ga bayyana matakan kar ta-kwana kan wata isakar mai zafin gaske da ke shirin tunkaro nahiyar daga Afirka.

Poland | Tsananin zafi
Poland tsananin zafiHoto: Aleksander Kalka/IMAG

Koriya ta Kudu da Japan da Canada su ma na daga cikin kasashen da ke dandana kudarsu a wannan shekara, yankin Agadez da ke tsakiyar hamadar Nijar ma ba a barshi a baya ba, ya fuskanci tsanain zafin da ya haura da maki 47 a baya-bayan nan lamarin da ka iya hadasa cututtuka da dama.

Masana dai na ba da shawarar kara ta'ammali da ruwa da cin abinci wadatacce a yanayin zafi, tare da kaucewa shan barasa, sai dai har yanzu ba a kai ga kayyade adadin ma'aunin nawa ne ke iya zama tsanain zafi daga wani yanki zuwa wanin ba, sai dai a Faransa ga misali, da zarar ma'aunin zafi ya haura 32, masana na cewa an shiga yanayi na tsanain zafi ke nan.