Zaftarewar dusar kankara ta rufta da sojojin Pakistan
April 7, 2012Sojojin Pakistan fiye da dari daya (100) ne zaftarewar dusar kankara ta binne a wani sansaninsu dake Gayari a yankin Himalaya wanda ke kan iyaka da kasar India a wannan Asabar. Lardin Siachen dake arewaci shine zirin da ya raba yankin Kashmir inda kasashen biyu na Indiya da Pakistan suka dade suna takaddama akansa kowa na cewa yankinsa ne. Wasu rahotanni sun ce yawan sojojin da dusar kankarar ta rufta da su sun kai 150. Kakakin rundunar sojin Manjo janar Athar Abbas yace an tura ma'aikatan ceto zuwa yankin a jiragen sama masu saukar ungulu domin kai dauki. Manjo janar Abbas ya ce ba'a sami wani labari ba game tabbacin ko akwai wadanda suka tsira da rayukansu. A cikin wata sanarwa Firaministan Pakistan Yousuf Raza Gilani ya baiyana kaduwa da aukuwar lamarin.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Saleh Umar Saleh