Zaman dari-dari dangane da barkewar rikici
September 14, 2017Har yanzu zaa iya cewar akwai zaman dar dar da rudami a wasu sassa da 'yan rajin Biafra sukai arangama da dakarun Soji a yankin kudu maso gabashin Najeriya da kuma a Jahar Rivers da ke yankin Niger Delta,inda yanayin ya kai ga afkawa kabilar Arewacin Najeriya da ke harkokinsu a Yankunan Biyu na kudu din.
Gararin baya bayannan din dai yai jallin salwantar rayuka da dukiyoyi,koda yake kawo yanzi akwai jamian tsaran Soji da Yan Sanda na sintiri.
Jim kadan dai bayan dakarun soji sun tarwatsa wasu kwajerin gwanon motoci da ke dauke da Yan rajin na biafra da ke kan hanyarsu zuwa garin jagoran kungiyar rajin Biafra din ta IPOB wato NNAMDI MAZI kANU,sai nan da nan Yan rajin na Biafra kama daga shiyyar Umuahia da Aba a jahar Abia da kuma yankin Obigbo da ke gab da shiga Birnin Fatakwal suka fara afkawa Alummar Hausawa yan Arewa da ke harkokinsu a wadannan sassa,kuma afkawar alkaluma sun tabbatar akwai salwantar rayuka da Dukiyoyi.
Wannan matafiyi ne daga Arewacin Najeriya ,kuma isarsa yankin na Igbo ta rutsa da shi.
Ahmad Dile,da shi kuma mai safara ne ya bayyana halin da suka shiga daga jiya din da wannan garari ya somo.
Yanzu dai Gwamnatin Jahar Abia da ananne gararin yafi tsanata ta kafa dokar ta baci kan zirga zirgar jamaa daga 6 na yamma zuwa shida na safe har kwanaki uku.
Yanzu kuma Kungiyoyin kabilar Igbo kwata ta Ohanaeze ,da ta bangare fafutukar kafa Biafra ta Biafra Zionist Federation da Sanatocin su sun bayyana matsayinsu kan wannan yamutsi,inda Ohanaeze da Sanatocinsu sukai kira da tsahirta kewayen da Soji ke yiwa gidan Nnamdi Kanu tare da kawo karshen cin zarafin Kabilar Igbo,inda kuma Biafra Zionist Movt ta bada waadin awoyi 48 na Soji su fice daga yankin na Igbo.
Yanzu dai da alammura suka lafa ,an nunar Gwamnoni biyar na yankin na Igbo sun kafa wani kwamitin bincika wannan garari da ya afku.Haka kuma Kungiyar mabiya Cocin Pentakostal a Kasar tai kira ga Gwamnatin Najeriya da a hanzarta tattaunawa kan yadda Kasar ke tafiya a gwamnatance da a siyasance.
Wani Mai wada dai a Jahar ta Abia da ke shugabantar Matasa ya bayyana min halin da ake ciki kawo yanzu.
Madawakin Fatakwal,Alh Yakubu dan Biafra tarihi ya dauko mai kukan kucciya kan zamantakewar Najeriyar mai jibi da gararin da ake ciki yanzu din.
Tuni dai yanzu Kungiyar masu safarar kayayyakin masarufi daga Arewa zuwa kudu maso gabashin Najeriyar suka sanar min cewar suna nan suna tuntubar juna kan matakin da zasu kai ga dauka dangane da safarar kayayyakin abinci yankin,bisa laakkari da yadda rayuwar direbobi da kayayyakinsu ke zama cikin hadari a shiyyar ta Igbo.
Muhammad Bello,DW Hausa Niger Delta.))