Zaman makoki a Jamhuriyar Nijar
June 26, 2024Sanarwar ta ce baya ma ga mutanen 21 da suka rasu cikinsu farar hula guda, wasu sojojin kuma guda tara sun samu raunuka a wannan hari da ya wakana a wajejen garin Tassia a Kudancin Banjo a cikin gundumar Tera jihar ta Tillabéri da ke wannan yanki na iyakoki uku na Nijar Mali da Burkina Faso, sannan maharan sun lalata motocin soja biyu, sai dai kuma duk da shammatar da aka nyi musu, sojojin cikin njajircewarsu sun yi raga-raga da maharan da dama tare da ababen hawansu wanda ba da jimawa ba aka tayar da jirage domin bin sauran yan ta'addan da suka gudu don ganin ba su samu kai labari ba. Ta haka ne ganin girman matsalar gwamnatin Nijar ta ayyana zaman makoki daga wannan rana ta Laraba domin juyayin rashin da aka yi tare da mayar da hankali ga yin addu'o'i na samun zaman lafiya a kasar. Sai dai a cewar masu sharhi kan harkokin tsaro a kasar ta Nijar irinsu Abas Abdoulmoumouni ya ce yunkurin samar da hanya tun daga gandun daji na Parc du W zuwa yankin ruwan Guinea ne ya sanya 'yan ta'addan da ke samun wani babban goyon baya ke kara kaimi wajen hare-haren.
Karin Bayani: 'Yan bindiga a Jamhuriyar Nijar sun hallaka jami'in gwamnati
Wannan matsala dai ta neman samun kwaro kaman yadda masana suka ambato don ganin yan ta'addan sun samu jin dadin cin karansu ba babbaka ya kuma hadu da wasu matsalolin inda wasu ke amfani da wannan dama domin habbaka harkokinsu na neman kudade ko kasuwanci kaman yadda Hama Oumarou dan kungiyar farar hula na jihar Tillabéri ya tabbatar.
Tun dai da dadewa masana sun yi ta bada shawarwari don ganin cewa an yi amfani a hannu daya da fusa'o'i na tattaunawa da mataki na zahiri ga al'umma domin kawo karshe matsalar ko kuma rage karfinta. A wata sanarwa da suke fitarwa na ayyukan da suke yi na yaki da ta'addanci a fadin kasar ta Nijar, rundinar sojojin kasar ta Nijar ta sanar bda kashe wani hatsabibin dan ta'adda mai suna Abdoulaye Souleymane Idouwal, da ker da babban ntasiri a wannan kungiya ta IS a yankin Sahel inda aka kashe shi a wani yanki kusa da Méhana cikin jihar ta Tillabéri. A ziyarar da yakai a Burkiuna Faso shugaban kasar na mulkin soja na Mali ya jaddada aniyar kasashen kunbgiyar AES na yakar ayyukan ta'addanci.