1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Fara shari'ar masu yunkurin juyin mulki

July 2, 2024

A Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, kotu tana ci gaba da shari'ar da ta shafi yunkurin juyin mulki da ake tuhumar mutane 51 da kitsawa ranar 19 ga watan Mayun 2024. An dai shaida wa mutanen laifuffukan da ake tuhumarsu.

https://p.dw.com/p/4hmdO
Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango
Yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Jean-Noel Ba-Mweze/DW

Kotun ta fara sauraron bahasi tare da gudanar da tambayoyi a wani zaman shari'a da take yi a gidan yarin sojoji na babban birnin kasar Kwango wato Kinshasa. Wannan zaman kotun ya kasance na biyar a shari'ar da ta shafi mutane 51 da ake tuhuma da laifin kai hari a gidan kakakin majalisar dokoki Vital Kamerhe da kuma fadar shugaban kasar Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango Félix Tshisekedi. Tuni ma Youssouf Ezangi, wani dan Birtaniya dan asalin Kwango da aka gabatar a matsayin mai daukar wadanda suka kai harin aiki ya yi watsi da tuhumar da ake masa. Shi dai dan shekaru 53, Youssouf Ezangi bai yarda cewa ya gana da Christian Malanga da zummar kitsa yunkurin juyin mulki ba. Amma ya ce sun hadu a Birtaniya da Switzerland da Angola a shekarun baya, lamarin da ya ba su damar kafa wata kungiya a Bandundu da ke yammacin kasar.

Karin Bayani: Bayan yunkurin juyin mulki

Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango
Kotun soja ta Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Jean-Noel Ba-Mweze/DW

A ranar 19 ga watan Mayun 2024 ne, DR Kwango ta fuskanci abin da sojojin kasar suka bayyana a matsayin yunkurin juyin mulki, lokacin da wasu mutane 12 suka kai hari a wasu manyan gine-gine da cibiyoyi na gwamnati. Sai dai Youssouf Ezangi da ke zama daya daga cikin wadanda ake tuhuma da wannan danyen aiki ya ce an gayyace shi zuwa wadannn wuraren, ba tare da bayyana masa ainihin dalilin zuwa cibiyoyin ba.

Ana tuhumar wadanda aka kama da aikata laifukan da suka shafi ta'addanci da mallakar makamai da albarusai ba bisa ka'ida ba da hada baki don aikata kisan kai da kuma tallafa wa ayyukan ta'addanci. Daga cikin wadanda ake tuhuma da yunkurin juyin mulkin na Kwango har da 'yan kasashen waje da suka hada da Amurkawa uku da dan Beljiyam da dan Birtaniya da kuma dan kasar Kanada.

Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango
Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Samy Ntumba Shambuyi/AP Photo/picture alliance

A ranar 5 ga watan Yuli ne za a ci gaba da zaman shari'ar, inda za a yi ma wadanda ake tuhuma tambayoyi ciki har da Amurkawa uku. Dukkanin mutane 51 da ake tuhuma ciki har da mata hudu na tsare a gidan yarin sojoji na Ndolo da ke birnin Kinshasa, bayan da kotu ta yi watsi da bukatar yi musu sakin talala. Idan aka same su da laifukan da ake zarginsu da aikatawa, za a iya yanke musu hukuncin kisa, a cewar kotun soji ta Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.