1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman tankiya tsakanin Rasha da Ukraine

Suleiman Babayo ATB
January 28, 2022

Gabashin Turai na ci gaba da zama karkashin rashin tabbas, inda ci gaba da zaman tankiya a gabashin Turai kan yuwuwar Rasha za ta yi kutse a Ukraine.

https://p.dw.com/p/46FFn
Ukraine Kiew Alltag Bus Fahrgast
Hoto: Sergei Chuzavkov/SOPA/picture alliance

Shugaba Volodymyr Zelenskiy ya bayyana yuwuwar kara samun sabani da kasar Rasha, amma ya soki yadda ake kammama yayin da ake ciki kan barkewear yaki salamakon yadda Rasha ta tura kimanin dakaru 100,000 iyaka da kasar ta Ukraine. Ya yi kalaman bayan Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya ce Amirka da kungiyar tsaron NATO ba su cika muradun magance matsalolin gabashin Turai da suka janyo yanyin da ake ciki ba, amma yana shirye da ci gaba da tattaunawa.

Rasha ta kuma ce ba ta da shirin fara yaki a gabashin Turai.

Kasashen Turai da Amirka na neman tabbatar da ganin hanyarsamar da makamashi ga kasashen na Turai yayin da ake ci gaba da zaman tankiya kan yuwuwar Rasha za ta yi kutse a Ukraine.