Zan yi aiki da kowa don gina kasa - Bazoum
March 22, 2021A daren jiya ne kotun tsarin mulki ta Jamhuriyar Nijar din ta tabbatar da zaben da aka yi wa Bazoum Mohamed na jam'iyyar PNDS Tarayya a matsayin shugaban kasa.
Shugaban kotun tsarin mulkin Bouba Mahaman ya yi inda ya ce Bazoum Mohamed ya samu wato kaso 55,66 daga cikin dari a yayin da Mahaman Ousmane ya samu kaso 44,34 daga cikin dari na kuri’un da aka kada.
Tuni dai sabon zabebben shugaban kasar ta Nijar Bazoum Mohamed ya bayyana farin cikinsa da kuma godiyarsa ga 'yan kasa tare ma da shan alwashi yin aiki tukuru wajen inganta rayuwar 'yan kasar.
Bazoum din har wa yau ya yi kira ga aboklin hamayyarasa Mahaman Ousmane da ya rungumi kaddara ya ba shi hadin kai su gina kasa tare, inda ya ce zai neme shi don samun shawarwari kan matakan da za a bi wajen ciyar da kasa gaba
A ranar 2 ga watan Afrilun da ke tafe ne dai za a rantsar da Bazoum Mohamed a matsayin shugaban kasa mai cikakken iko inda zai yi wa'adi na tsawon shekaru biyar.