SiyasaAfirka
Al-Azahar na son Faransa ta daina zanen barkwanci
November 9, 2020Talla
A taron da ministan Faransan ya yi da jiga-jigan malaman Musulumci na kasar Masar ya jaddada cewa kasarsa ba ta yaki da Islama, kuma ya je Masar ne domin nuna wa Larabawa irin kimar da Faransa ta ke kallon Musulumci da ita.
Sai dai Sheik Ahmed al-Tayeb babban jagoran cibiyar nazarin Islama ta Al-Azhar ya ce ko kadan wannan ziyara ba ta canza matsayarsu kan dole Faransa ta martaba addinin Islama ba, yana mai cewa batanci ko danganta wani abu mara kyau ga Manzon Tsira (S.A.W) a musulumce babbann zunubi ne, a don haka duniyar musulmi za ta yaki irin wannan abubuwa da Faransa ta yi har zuwa kotun duniya koda za su karar da rayuwarsu a neman adalci a wannan magana.