1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga a Aljeriya

May 10, 2019

Daruruwan 'yan kasar Aljeriya ne suka dafifi a Algiers babban birnin kasar a makonsu na 12 a jere na zanga-zangar adawa da manufofin gwamnati da ke mulki.

https://p.dw.com/p/3IHzy
Algerien Massenproteste gegen Regierung
Hoto: Getty Images/AFP/R. Kramdi

Boren nasu na wannan Juma'a, bore ne na bukatar hukumomi su gaggauta sakin jagorar adawar kasar Louisa Hanoune wadda ke tsare a gidan yari.

A ranar Alhamis ne dai kotun sojin kasar ta bayar da umurnin tsare jagorar ta adawa, kan laifin da ba a bayyana ba.

Hukumomin kasar ba su bayar da wasu cikakkun bayanai kan tsare matar 'yar shekaru 65 ba, wacce ta yi kaurin suna wajen sukar tsohon shugaban kasar Abdulaziz Bouteflika.

Ana dai zargin kama ta da aka yin, da alaka da kamen wasu dangane da tsohon Shugaba Bouteflika.