Zanga-zanga a birnin Frankfurt
May 19, 2012A Jamus dubban mutane ne ke gudanar da zanga-zanga a birnin Frankfurt domin nuna adawa da tsarin aikin bankunan da kuma matakan tsuke bakin aljihu da Kungiyar Tarayyar Turai ke dauka. Masu gudanar da zanga-zangar a cibiyar aikin kudin na Frankfurt sun hada ne da kungiyoyin kodago da jam'iyyun siyasa da kuma sauran kungiyoyi masu zaman kansu. Wadanda suka shiyar zanga-zangar sun ce mutane dubu 25 ne suka hallara a yayin da 'yan sanda kuma suka ce zanga-zangar ta samu halarcin mutane dubu 20. Zanga- zangar ta yau ta samu rakiyar 'yan sanda masu yawa tun bayan fara ta kwanaki uku da suka gabata. Masu zanga- zangar dai na yin kira ne da a kawo karshen tsarin aikin babban bankin Turai. Ko da ya ke zanga-zangar tana gudana a cikin limana to amma an samu wasu 'yan rikice rkice da ba a rasa ba.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Usman Shehu Usman