Zanga-zangar adawa da matakin 'yan Taliban
September 14, 2021Talla
Dubban mutane sun gudanar da zanga-zanga a birnin Kandahar da ke kudancin Afghanistan, a ci gaba da nuna rashin jin dadi kan matakin sabbin mahukuntan kasar na cewa su fice daga sansanin sojan yankin da suke samun mafaka.
An gudanar da zanga-zangar ne a harabar ofishin gwamnan Kandahar din, kana kuma wasu hotunan bidiyo sun nuna yadda masu boren suka toshe manyan hanyoyi a birnin.
Har yanzu da akwai mutane akalla dubu uku da suka ha da dangi da iyalan sojan tsohuwar gwamnatin Afghanistan da ke ci gaba da zama a sansanonin sojan na Kandahar, inda rahotanni ke cewa kungiyar Taliban ta ba su wa'adin kwanaki uku kacal dan su fice daga sansanin. Sai dai kawo yanzu kungiyar ta ba kara cewa uffan kan wannan batun ba.