Zanga-zanga a Faransa ta yi ƙamari
April 29, 2016Talla
Masu yin gangamin sun cina wuta a wurare da dama tare da ƙone motoci a biranen Paris da Nantes da Rennes da kuma wasu sauran yankunan.'Yan sanda sun cafke mutane kusan 124 yayin da wasu sama da 50 sun jikkata a ciki har da 'yan sanda 24.Ministan cikin gida na Faransa Bernard Gazeneuve ya yi tsokaci a kan lamarin.
''Ina yin Allah wadai da babbar murya a game da wannan ta'adi na farfasa gine-gine da ƙone ƙone da masu yin gangami suka yi.''Watannin biyu ke nan da suka wuce da ma'aikata da ƙungiyoyin suke yin zanga-zanga a Faransar a kan dokar da gwamnatin ta amince da ita a kan ma'aikata wadda 'yan ƙwadagon ke cewar tana nuna fifiko ga waɗanda suka mallaki kamfanoni da masana'antu.