Zanga-zanga a Ukraine
April 1, 2007Dubun dubunnan al´ummomin ƙasar Ukraine sun shirya zanga-zanga, bisa gayyatar jama´iyun adawa, da ke bukatar shugaba Viktor Iyukacenko, ya rusa majalisar dokoki, sannan ya shira zaɓe domin hidda ƙasa daga ƙangin siyasar da ta tsinci kanta ciki.
Rahottani daga Kiev, babban birnin ƙasar sun ce, wannan shine taron gangami irin sa na farko, tun bayan wanda ya wakana a shekara ta 2004, wanda kuma yayi sanadiyar zuwan Shugugaba Iyukacenko, kan hawa kankaragar mulki.
Yan adawar, bisa jagorancin Praminista Viktor Iyanukovitch, sun sha alwashin sai sun ga abinda, ya turewa buzu naɗi, a game da wannan bukata da su ka bayyana.
A nasa gefen shugaban ƙasa, ya alkawarata ganawa gobe da shugaban Majalisa, da na runkunnan jam´iyu a majalisar, a game da wannan batu.
Saida masu nazarin harakokin siyarsar ƙasar, na hasashen cewar, da zarna ya kuskura, ya shirya zaɓen, jama´iyar sa ba za kai labari ba.