1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga kan baki ta yi zafi a Jamus

September 1, 2018

Masu akidar kyamar baki a Jamus sun nuna matsayinsu a gabashin birnin Chemnitz bayan kisan wani dan kasa da aka yi.

https://p.dw.com/p/34A1y
Deutschland | Rechte Demo in Chemnitz
Hoto: picture-alliance/dpa/R. Hirschberger

Wasu masu adawa da tsarin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na karbar baki, sun yi wata zanga-zanga a gabashin birnin Chemnitz, don nuna bacin rai kan kisan da wasu baki suka yi wa wani Bajamushe dan kasa.

Zanga-zangar da masu adawar suka yi, ta gamu da wani ayarin da shi kuwa ke goyon bayan manufar Angela Merkel din a wannan Asabar.

'Yan kungiyar nan ta PEGIDA masu kyamar baki da 'yan jam'iyyar AfD su ma da ke da akidar ce ke nuna fushin, yayin da su kuwa masu goyon karbar bakin na Angela Merkel ke cewa kauna dai ba kiyayya ba a Jamus.

Ko makon jiya ma dai sai da wasu daruruwan masu kyamar bakin suka nuna fushinsu kan wasu mutane biyu da ake tsare da su, 'yan asalin Iraki da kuma Siriya kan zargin kisan Bajamushen.

Jam'iyyun siyasa da kungiyoyi da dama suka yi kiran a fito don macin nuna kauna maimakon kiyayya ga bakin.

'Yan sanda dai sun ce ba a wuce makadi da rawa ba a zanga-zangar.