1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zimbabuwe: Mutane 68 sun jikkata

Abdul-raheem Hassan
January 17, 2019

Akalla fararen hula 68 na cikin mawuyacin hali sakamakon barkewar mumunar zanga-zangar adawa da gwamnati kan karin farashin man fetur.

https://p.dw.com/p/3BgV3
Simbabwe Harare Benzinkrise Ausschreitungen
Hoto: Reuters/P. Bulawayo

Kungiyar likitoci a Zimbabuwe ta ce tun farkon wannan mako likitoci na fama da majinyata a asibitocin gwamnati da masu zaman kansu, inda mutane 172 ke jiya bayan tashe-tashen hankula da suka barke a kasar. An zargi jami'an tsaro da kai samame kan 'yan adawa da ke sukar manufofin gwamnatin Shugaba Emmerson Mnangagwa. Tun dai bayan kawo karshen shugabancin tsohon shugaban kasar Robert Mugabe, 'yan kasar Zimbabuwe na kokawa da yadda al'amura ke tafiya a kasar.