Boren kin sabon shugaban hukumar zabe a Kwango
July 8, 2020Wata sabuwar zanga-zanga ta barke a sassa daban-daban na kasar Jamhoriyar Dimukaradiyar Kwango sakamakon wani yunkuri da gwamnatin kasar ta yi na nada Ronsard Malonda a matsayin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar CENI. Malondan dai ya yi kaurin suna wajen kwarewa kan murde zabe da tabka magudi.
Majalisar dokokin ta Kwango wadda magoya bayan tsohon shugaban kasar Joseph Kabila ne ke da rinjaye, ta yanke shawarar nada Ronsard Malonda a matsayin shugaban hukumar. Sai dai jam'iyyun adawa da kungiyoyi masu zaman kansu a Goma babban birnin lardin Kivu ta Arewa da kuma birnin Kisangani da ke yankin Tshopo arewa maso gabacin kasar.
Ya zuwa yanzu dai 'yan sanda sun kama masu zanga-zangar sama da 47 a biranen guda biyu, amma shugaban 'yan sandan kasar Van Aba ya ce tuni aka sallami masu zanga-zangar.
Kungiyoyin adawar sun yanke shawarar ci gaba da zanga-zangar muddun shugaba Felix Tshisekedi na kasar ya yi yunkurin tabbatar da kudirin 'yan majalisar.