Aljeriya ta nuna fargabar sake shiga yakin basasa
March 1, 2019Jam'iyyun adawa da kungiyoyin masu fafutika a kasar Aljeriya sun jagorancir zanga-zangar gama gari a kasar, don nuna adawa da sake tsayawar takarar shugaban kasar, Abdel-Aziz Bouteflika, karo na biyar, babban hafsan sojin kasar ya yi gargadin jefa kasar cikin yakin basasa, makamancin wanda aka taba yi a kasar a shekarar 1991.
Jami'o'i da dalibansu sun amsa kiran zanga-zangar gama garin dake adawa da matakin tazarce karo na biyar da shugaba Butifilikan key i karo na biyar ke nan, wasunsu suka dauke da akwatunan daukar gawa da ke alamta sallar gawa ga mulkin Bouteflika, zanga-zangar da sannu-sannu take rikidewa zuwa ta neman sauyi.
Ita kungiyar 'yan jaridar kasar, dama kananan ma'aikatan da ke aiki a kafofin watsa labaran gwamnati, sun bi sahun masu zanga-zangar, suna masu alwashin bayyana wa 'yan kasa gaskiyar abin da ke wakana.
Tuni dai gamayyar jam'iyun adawa a kasar, suka fara wani kudirin doka da zai takaita wa'adin mulki a kasar, duk kuwa da cewa, sun sai zai yi wuya majalisar da jam'iyya mai mulki ke da rinjaye ta amince da kudurin.
Idan dai ana iya tunawa, a shekarar 1991 ne sojojin kasar ta Aljeriya, suka soke zaben da masu kishin Islama suka lashe, lamarin da yakai ga barkewar yakin basasa da yakai ga halaka dubun-dubatan 'yan kasar.