Zanga-zanga ta rikide zuwa yamutsi a Iran
January 2, 2018Zanga-zangar wadda aka fara a ranar Alhamis da ta gabata a garin Mashhad, wanda shi ne na biyu mafi girma a kasar ta Iran, kuma babban sansanin 'yan adawar shugaban kasa Hassan Rouhani, ta kuma bazu zuwa sauran manyan biranen kasar, ta zama mafi girma da aka taba gani, tun bayan boren da ‘yan kasar suka yi a shekarar 2009, kan neman sauya tsarin shugabancin kasar.
Akwai fargabar cewa wannan bore zai ci gaba da yin kamari, idan aka yi la'akari da kiran da jagororin masu zanga-zangar ke yi na zafafa zanga-zangar, wacce sannu sannu ke rikidewa yamutsin da ya kai ga samun asarar rayuka. Kimanin mutane 22, cikinsu hadda jami'an tsaro biyu, a yayin wata arangamar da daruruwan masu zanga-zanga dauke da makamai suka yi da jami'an tsaron kasar, a lokacin da suka yi yunkurin kwace iko da wasu ofisoshin ‘yan sanda da kuma barikokin soji.
Shugaban kasar Hassan Rouhani, wanda ya ce 'yan kasar na da 'yancin yin zanga zangar lumana, kuma a shirye yake ya saurari kokensu don magancesu, ya zargi Amirka da Birtaniya da Saudiyya da kitsa yamutsin, yadda dubban magoya bayansa suma sukai nasu tattakin nuna kyama ga wadanda suka kira makiyan tsarin Musuluncin da kasar ke bi.
Masharhanta kan lamuran Gabas ta Tsakiya sun yi amannar cewa, zanga-zangar ta yi matukar yiwa gwamnatin ta Iran ba-zata, ganin yadda duk da karancin masu sanya hannayen jari a kasar, tattalin arzikinta ya fara bunkasa, bayan da ta cimma yarjejeniyar nukiliya da kasashen Yamma, aka kuma dage mata takunkumi, kamar yadda karfi iko da fada ajinta a yankin ke karuwa. To sai dai 'yan kasar ba kasafai suke cin moriyar wannan bunkasar tattalin arzikin ba, yadda ake kashe makudan biliyoyi wajen tallafawa Hizbullah da Hamas, da kuma yaki a Siriya da Yemen da Iraki, baya ga biliyoyin da take kashewa wajen yada akidar Shi'a a sassan duniya.