Zanga-zangar adawa da Al-Shabab a Kenya
April 7, 2015Daruruwan dalibai a yau Talata sun gudanar da maci a birnin Nairobi, fadar gwamnatin kasar Kenya, dan nuna girmamawa ga 'yan uwansu da kungiyar al-Shabab suka halaka. Inda suke kira ga gwamnati ta kara tsaurara matakan ba su kariya, adai-dai lokacin da 'yan ta'addan ke ci-gaba da zubar da jinin al'umma.
Gangamin daliban dai ya haifar da cinkoson ababen hawa, biyo bayan yadda suka suke zaman dirshan a kan wasu titunan, inda suke hana masu ababan hawa shigewa.
Masu zanga-zangar dai, sun rika tofin Allah tsine ga 'yan ta'addan na al-Shabab wadanda suka dauki alhakin kai harin na jami'ar Garissa. Inda suka halaka mutane 148 a arewa maso gabashin kasar ta Kenya. Wasu daga cikin daliban kuma ke cewa sun gaji da ayyukan rashin imanin na al-Shabab.
Har ila yau masu zanga-zangar sun bukaci mahukunta a kasar ta Kenya da su biya diyya ga 'yan uwan mamatan.
A wani labarin kuma wata kotu a birnin Nairobi ta bada umarni a ci gaba da tsare wasu mutane biyar 'yan Kenya da wani dan Tanzaniya, tsawon kwanaki 30. Hakan dai 'yan sanda za su sami damar gudanar da bincike, don gano ko suna da alaka da harin da aka kai kan dalibai a jami'ar Garissa da ke kasar ta Kenya.