1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar adawa da ballewar Kataloniya

Ramatu Garba Baba
October 29, 2017

Daruruwan mutane sun gudanar da zanga-zanga a birnin Barcelona na kasar Spain don nuna adawa da yunkurin neman ballewar yankin Kataloniya daga kasar.

https://p.dw.com/p/2mi9b
Spanien - Demonstrationen für die Einheit von Spanien und Katalonien in Barcelona
Hoto: Reuters/Y. Herman

Wadanda suka shirya gangamin na wannan Lahadin sun ce sun yi hakan ne a wani mataki na nuna hadin kai da kuma fatan kasancewa kasa Spain guda dunkulalliya. Mutane akalla miliyan daya ne suka shiga gangamin  dauke da alluna masu rubuce-rubuce na adawa da duk wani yunkurin na raba Kataloniya da kasar Spain.

A ranar Asabar ne gwamnatin Spain ta sanar da  karbe madufan iko a yankin Kataloniya mai kwarya-kwaryar 'yancin kai ya soma aiki inda Fraiministan Mariano Rajoy ya kuma ce za a gudanar da zabe a watan Disamba.

Gwamnatin Madrid ta ce hambararren shugaban na Kataloniya na iya shiga takara a zaben yankin da za'a gudanar a watan Disamba. Baya ga wasu 'yan kasar masu adawa da batun ballewar, kasashen Turai da Amirka suma sun nuna adawarsu da ballewar yankin na Kataloniya daga Spain, bayan kuri'ar neman ballewar da al'ummar yankin suka kada.