1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar adawa da kyamar baki a Jamus

Yusuf Bala Nayaya
October 13, 2018

Dubban al'umma sun gudanar da zanga-zangar adawa da kyamar baki da nuna wariya a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus, sakamakon karuwar kyama ga baki da ake samu a wasu yankunan kasar.

https://p.dw.com/p/36UDx
Berlin - Proteste gegen die AFD in Berlin
Hoto: picture-alliance/abaca/E. Basay

Wannan zanga-zangar da ke zuwa ta wannan Asabar na zuwa yayin da ake fargabar cewa masu kin jinin baki na kara yawa da karin karfin gwiwa a kasar.

Akwai kungoyoyi da dama da suka fita wannan zanga-zanga da suka hadar da kungiyoyi na mabiya addinin Islama da kungiyoyi masu maraba da baki da masu fafutukar kare auren jinsi.

Cikin wadanda suka mara baya ga wannan gangami har da minisatan harkokin wajen Jamus Heiko Maas, da ke ganin abin farin ciki shi ne mafi akasari al'ummar Jamus na maraba da baki, ba sa nuna wariya.