Zanga-zangar adawa da wariyar launin fata a nahiyoyi biyar
Abin da ya faru da George Floyd a Minneapolis ya tayar da hankalin al'umma a duniya. Duk da annobar cutar coronavirus, dubban jama'a sun fita sun yi zanga-zangar adawa da wariyar launin fata.
Paris: Zanga-zanga a Champ de Mars
A kwanakin da suka wuce, 'yan sanda a birnin Paris sun tarwatsa masu zanga-zanga tare da harba musu barkonon tsohuwa. Tun da farko hukumomi sun haramta zanga-zanga a dandalin Eiffel Tower da kofar ofishin jakadancin Amirka. Amma duk da haka dubban mutane sun bazama tituna domin nuna adawa da wariyar launin fata. Cin zarafi da 'yan sanda ke yi wa bakar fata ya yadu a garuruwa da dama a wajen Paris.
Liége: Zanga-zanga duk da haramci
Belgium kamar sauran kasashen Turai, ita ma tana da nata alhakin tursasawar 'yan mulkin mallaka da ci da gumin wasu nahiyoyi. Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongo ta taba zama mallakar Sarki Leopold na biyu wanda shi ne tushen kafa gwamnatin zalunci da rashin adalci. Zanga-zangar adawa da wariyar launin fata ta karade biranen Brussels da Anwerp da Liege, duk da an haramta saboda cutar coronavirus.
München: Launuka sun kawata Bayern
Daya daga cikin gangami mafi girma da aka yi a Jamus ya gudana ne a birnin Munich, inda mutane kimanin 30,000 suka yi dandazo. Akwai kuma gagarumar zanga-zanga da aka yi a biranen Cologne da Frankfurt da kuma Hamburg. A Berlin fadar gwamnatin kasar, 'yan sanda sun rufe titin Alexanderplatz saboda yawan mutanen da suka yi tururuwa zuwa taron gangamin.
Vienna: Mutane 50.000 suka fito zanga-zangar adawa da wariya
Mutane 50,000 ne suka hadu a Vienna babban birnin Ostiriya a ranar Jumma'a. A daya daga cikin zanga-zanga mafi girma a 'yan shekarun baya-bayan nan, makamancin gangamin da ya kawo karshen badakalar siyasa ta Ibiza ta gwamnatin kama-karya ta kawancen 'yan ra'ayin rikau a 2019. An rubuta Kalmar "Black Lives Matter" wato rayuwar bakar fata na da muhimmanci, a jikin wata motar 'yan sanda.
Sofia: Zanga-zangar mutane fiye da 10 ta adawa da wariyar launin fata
Kamar wasu kasashen Turai da dama, a yanzu haka Bulgaria ta haramta tarukan da ya wuce na mutane 10. Sai dai duk da haka, daruruwan mutane sun yi fitowar dango a birnin Sofia suna fadin kalmar George Floyd ta karshe: "Ba na iya numfashi." A waje guda kuma suna jawo hankali ga akidar wariya a tsakanin al'umma a Bulgeriya.
Turin: Zanga-zanga a lokacin coronavirus
Wannan matar da ke garin Turin, ta furta damuwarta sanye da kyallen rufe baki da hanci saboda cutar coronavirus. A Italiya ma taken "Black Lives" na daukar hankali. Zanga-zangar da aka yi a biranen Rome da Milan, ga alama sune mafi girma da aka gani a Italiya tun bayan da aka dauki matakan yaki da corona. Italiya na daya daga cikin manyan kasashen Turai da ke karbar 'yan gudun hijira daga Afirka.
Lisbon: Dauki mataki yanzu
"Dauki mataki yanzu," shi ne taken wadannan masu zanga-zangar a Lisbon babban birnin kasar Portugal. Ba a ba su izinin yin zanga-zangar ba, to amma 'yan sanda sun kyale su. A Portugal ma 'yan sanda na yawan cin zarafin bakar fata. A lokacin wata zanga-zanga da aka yi a watan Janairun 2019, 'yan sanda sun harbe su da harsasan roba.
Kasar Mexico: Floyd da Lopez
A Mexico ba mutuwar George Floyd ce kadai take damun kasar ba, har ma da makamancin wannan hali da wani birkila Giovanni Lopez ya samu kansa a ciki. A watan Mayu 'yan sanda sun kama shi a jihar Jalisco da ke yammacin kasar saboda rashin sanya takunkumin rufe baki, kuma a karshe ya mutu sakamakon azabtarwar da 'yan sanda suka yi masa.
Sydney: Wariyar launin fata akan 'yan Aborigines
Zanga-zangar ta Sydney ta fara da tayar da wani bakin hayaki na al'ada. Goyon baya da mutane kimanin 20,000 da suka fito zanga-zangar suka nuna ba kawai ga George Floyd ta tsaya ba, har ma ga sauran 'yan Ostraliya 'yan kabilar Aborigin wadanda suka sha fuskantar tarzomar 'yan sanda. Masu zanga-zangar sun nunar da cewa bai kamata a bari wani dan kasarsu ya mutu yana tsare a hannun 'yan sanda ba.
Pretoria: Daga hannu sama a dunkule
Daga hannu sama da dunkule 'yan yatsu, inkiya ce ta maudu'in #BlackLivesMatter. Ko da yake an dade ana amfani da wannan alama. A lokacin da gwamnati ta sako dan fafutukar 'yancin Nelson Mandela daga gidan yari a watan Fabrairu 1990, ya daga hannunsa sama a fafutukarsa ta samun 'yanci, kamar yadda wannan dan zanga-zangar ya yi yanzu a Pretoria. Har yanzu ana fifita farar fata a Afirka ta Kudu