1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokar zama dan kasa ta harzika mutane a Indiya

Suleiman Babayo
December 16, 2019

Dubban mutane sun ci gaba da zanga-zanga kan sabuwar dokar zama dan kasa a Indiya ga wasu 'yan kasashe makwabta da ake ganin nuna wariya ga Musulmai.

https://p.dw.com/p/3Utku
Indien, Neu-Delhi: Protestierende Jamia Milia Islamia Studenten
Hoto: DW/A. Ansari

Dubban masu zanga-zanga sun mamaye titunan birnin New Delhi na kasar Indiya domin ci gaba da nuna takaici bisa sabuwar dokar da ake gani ta nuna wariya, domin ta amince duk 'yan kasashe makwabta na Pakistan, da Bangaladash, da Afghanistan idan suka shiga kasar bisa dalilan musgunawa tsirarun da ba Musulamai ba, za a ba su katin zama 'yan kasa, indn dokar ta ware ban da Musulman da suka fito daga kasashen karkashin wannan tanadi.

Tun makon jiya ake kai ruwa rana tsakanin masu zanga-zanga da jami'an tsaro bayan da majalisar dokokin kasar ta Indiya ta amince da ayar dokar mai haifar da cece-kuce. Ana zargin Firaminista Narendra Modi da aiwatar da wata manufa domin kara nuna tsangwama ga Musulman kasar kimanin milyan 200 da ke zama tsiraru yayin da ake zargin gwamnatin da manufofin irin na kishin 'yan Hindu.