1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane sun fusa da dauke wutar lantarki

Suleiman Babayo MAB
January 25, 2023

Dubban mutane sun shiga zanga-zangar matsalolin katsewar wutar lantarki da aka yi a birane da dama na kasar Afirka ta Kudu

https://p.dw.com/p/4MhNC
Afirka ta Kudu I Zanga-zanga
Afirka ta KuduHoto: ROGAN WARD/REUTERS

Dubban sun yi zanga-zanga kan titunan kasar Afirkia ta Kudu a wannan Laraba domin nuna takaici kan matsalolin makamashi na hasken wutar lantarki da ake samu lamarin da ke tabarbara lamura a kasra mafi ingancin tattalin arziki na zamani a nahiyar Afirka. Masu zanga-zangar sun yi dafifi a gine-ginen gwamnati a birnin Johannesburg da sauran biranen kasar.

Galibin masu zanga-zangar sun yi shiga kamar na jam'iyyar adawa ta DA wadda ta bukaci a gudanar da gangamin adawa da gwamnatin kasar karkashin jam'iyyar ANC.

Shugaba Cyril Ramaphosa na kasar ta Afirka ta Kudu a wannan makon ya bayyana cewa ya fahimci irin rashin jin dadi da mutane suke nuna bisa yanayin da kasra ta samu kanta, amma ya ce ba matsaloli da za a magance rana daya ba, domin haka ana bukatar hakuri.