1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar kare Islama a Pakistan

September 16, 2012

Daruruwan mutane sun gudanar da zanga-zangar ƙin jinin Amurka a gaban ofishin jakadancin Amurkan da ke Karaci, a ƙasar Pakistan.

https://p.dw.com/p/16A5S
Shite Muslim supporters of the Imamia Student Organization (ISO) shout slogans as they burn a U.S. flag during an anti-American demonstration in Peshawar September 14, 2012. Some 40 protesters gathered to take part in the protest to condemn a film being produced in the U.S. that insulted Prophet Mohammad. REUTERS/Fayaz Aziz (PAKISTAN - Tags: POLITICS CIVIL UNREST RELIGION)
Hoto: Reuters

Masu zanga-zangar sun ce sun yi hakan ne biyo bayan fim da aka nuna a Amurka da ke batanci ga addinin Islama wanda su ka ce cin fuska ne ga dukakan musulmi a duniya.

Yayin zanga-zanar dai, mutane sun yi ta jifan ofishin jakadanci Amurkan da duwatsu, lamarin da ya sanya jami'an tsaro tarwatsa su da hayaƙi mai sa hawaye da kuma ruwan zafi.

Mai magana da yawun wanda su ka shirya zanga-zangar, Liaquat Hussain ya ce mutum guda ya riga mu gaidan gaskiya yayin da wasu da dama su ka jikkata. Sai dai rundunar 'yan sandan Karacin ba su ce komai ba game da batun rasuwar mutumin.

A baya dai gwamnatin Pakistan da majalisar ƙasar sun yi tur da fidda fim ɗin wanda aka sanya a shafin internet na YouTube.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Halima Balaraba Abbas