Zanga-zangar kin jinin Amirka a Kano
September 22, 2012Daruruwan musulmi na birnin Kano da ke arewacin Tarayyar Najeriya sun gudanar da zanga-zangar yin Allah wadai da faifai bidiyo da aka wallafa a kasar Amirka wanda ya yi batanci ga addinin musulunci. Wata kungiyar 'Yan Shia'a ce ta kira wannan zanga-zanga a jihar da da ta kunshi musulmi miliyon hudu da dubu 500. Mutane dauke da tutocin Amirka da Isra'ila da kuma hoton Barack Obama ne suka yi taka sayyada har i zuwa fadar sarkin Kano Dr Ado Bayero da kuma babban masalanci cikin birni.
Cikin jawaban da wadanda suka jagorancin zanga-zangar ta Kano suka yi, sun yi kira da a kafa wata dokar kasa da kasa da za ta haramta wa kafafen watsa labarai cin zarafin addinai. Hakzalika sun yaba matakan da kiristocin Lebanon suka dauka na yin tofi llah tsine ga faifai bidiyon na kasar Amirka.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi