Zanga-zangar kin jinin gwamnatin Pakistan
August 16, 2014Talla
Masu aiko da rahotanni sun ce mutanen da yawansu yanzu haka ya kai kimanin dubu 20 na ta rera kalamai na kin jinin gwamnati kuma sun ce ba za su bar wajen ba har sai Sharif din ya yi murabus.
Da ya ke jawabi ga dubban magoya bayan jam'iyyarsa, tsohon dan wasan cricket din nan kana jigo a bangaren 'yan adawar kasar Imran Khan wanda ke kan gaba a zanga-zangar ya ce babu wata matsin lamba da za ta sanya su sauya matsayin da suka dauka.
Mr. Khan ya ce lokaci ya yi da al'ummar Pakistan za su yanke hukunci kan wannan gwamnatin da ba su amince da ita ba don suna bukatar adalci da 'yanci.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar