1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Boren adawa da jam'iyyar AFD

Binta Aliyu Zurmi
January 20, 2024

A Jamus sama da mutum 100,000 ne suka fantsama manya da kananan titunan biranen kasar suna masu tir da matakin jam'iyyar AfD mai tsattsauran ra'ayin kishin kasa na neman a fitar da masu neman mafaka daga kasar.

https://p.dw.com/p/4bVHM
Demonstrationen gegen Rechtsextremismus - Hannover
Hoto: Moritz Frankenberg/dpa/picture alliance

A birnin Frankrurt da ke zama cibiyar kasuwancin Jamus sama da mutum 35,000 ne suka fita boren, karkashin taken kare dimukuradiyya.

Al'umma daga birane sama da 100 ne manya da kanana suka fito domin nuna rashin goyon bayansu ga wannan jam'iyya da ta yi kaurin suna wajen kin jinin baki.

'Yan siyasa da shugabannin majami'u da shugabannin kungiyoyin kwallon kafa ta Bundesliga, sun yi kira ga Jamusawa da su tashi tsaye wajen yin tir wannan akida da jam'iyyar ta AFD ke da ita.