SiyasaAsiya
Manoman Indiya na shirin fadada zanga-zangarsu zuwa Delhi
March 4, 2024Talla
Dubban manoma ne suka fara tattakin da suka kira"Delhi Chalo" wanda ke nufin "Mu je Delhi" a watan da ya gabata, amma jami'an tsaro suka hanasu isa tun a nisan kilomita 200 daga arewacin babban birnin kasar ta hanyar amfani da hayaki mai sa hawaye da ruwan zafi.
Manoman da ke neman a kara farashin amfanin gonakinsu, sun tsananta zanga-zangar ne bayan gazawar tattaunawar da aka yi ta yi da su.
A ranar Laraba ne dai ake saran manoma daga jihohi daban-daban na Indiya, za su isa New Delhi kamar yadda wani shugaban kungiyar manona, Ramandeep Singh Mann, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.