1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar nuna adawa da mulkin Paul Biya a Kamaru

September 29, 2011

Wasu da ba'a san ko su wanene ba sun kai hari a kan 'yan sanda a Kamaru domin nuna adawa da mulkin Paul Biya

https://p.dw.com/p/12jFG
Shugaba, Paul BiyaHoto: AP

Wadansu 'yan bindiga masu sanye da kayan soja suna kuma dauke da wasu rubuce-rubucen da ke ga shugaba Paul Biya na Kamaru da ya sauka daga kujerar mulkin kasar ko ta halin kakak, sun toshe wata babbar gada suna harbin 'yan sanda na tsawon sa'oi da dama. To sai dai kafofin yada labaran kasar sun ce wasu 'yan kungiyoyin 'yan bindiga ne wadanda ba'a san ko su wanene ba. An dai yi ta jin karar harbin bindiga a Doula babban birnin cinikayyar kasar kuma tuni gwamnatin ta aika da dakarunta zuwa birnin domin su gudanar da binciken a kan duk motocin da ke wucewa. Wadanda su gane wa idanunsu sun shaida cewa an yi musayar wutar ne a gadar Vouri wanda akalla motoci dubu 35 suke amfani da shi a kowace rana.

Shugaba Paul BIya wanda ya ke kan karagar mulki tun shekarar 1982 zai kara da 'yan takara 22 a zaben da za'a gudanar ran 9 ga watan Oktoba mai kamawa kuma kawo yanzu kuri'ar jin ra'ayi na nuna cewa mai yiwuwa shugaban zai sake dawowa ya yi  wani wa'adin na shekaru bakwai

Mawallafiya: Pinado Abdu

Edita          : Umaru Aliyu